20 Agusta 2021 - 15:14
An Kashe Mutane Da Dama A Yayin Wani Turmutsitsi A lokacin Gudanar Da Zanga Zanga A Kasar Afghanistan

Rahotanni sun bayyana cewa An kashe mutane da dama a garin Asadabad dake Arewa maso gabashin kasar Afghanistan lokacin da dakarun kungiyar Taliban suka bude wuta kan wasu masu zanga- zanga da suka daga tutar kasar a ranar samun yanci da hakan ya jawo Turmustitsi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA : Wani shaidan ganin da Ido mai suna Mohammad Salim dake birnin Kunar ya shaida cewa ya zuwa yanzu babu tabbaci game da abin da ya haddasa turmutsitsi da kai ga rasa rayuka, A daura da haka kuma an kashe mutane 12 a gefen filin sauka da hawa jirgin sama na Kabul a dai dai lokacin da dubban Afganawa suke jiran a kwashesu daga kasar tun bayan kungiyar Taliban ta kwace mulkin kasar,yanzu haka dai darurwa Afganawa ne ke tsrewa daga kasar,

Ita dai kungiyar Taliban ta kwace mulkin kasar ne cikin ruwan sanyi bayan janye sojojin Amurka daga kasar, inda ta sanar da kafa gwamnatin musulunci ta Afghanistan, ana shi bangaren shugaban kasar Iran Ibrahim Ra’isi ya fadi cewa kasarsa a shirye take ta hada kai da kasashen Rasha da China wajen samar da zaman lafiya da tsaro a kasar ta Afghanistan.

342/